Table of Contents
Yadda ake hada Alkaki a saukake
Alkaki dai kamar yadda kowa ya sani yana daya daga fannin abinci wadanda ake cema snacks kuma daya ne daga cikin abuncin da ake amfani da alakma a matsayin babban abin sarrafawa, inda kamar wajen biki ko kuma ma hakanan a gida ana yin sa don a ci.
A dalilin haka ne a yau cikin yardar Allah zamu yi bayani akan yadda ake alkaki a saukake inda zamu lissafa kayan da ake sawowa a kasuwa wato kayan hadin da kuma matalkan da ake bi a wajen hada shi idande baa manta a baya ba mun kowa yadda ake hada cake inda muka koya shi kuma akwai Yadda ake alala Mai kwai in baa karanta ba ana iya dubawa suma.
kar a manta ana tare da website din Hausawasite.com.ng ne wanda ta Al’ummar Hausa ce inda ake koyon abubuwa daban daban daga masana da dama a cikin harshen hausa musamman sana’oi don dogaro da kai Domin kasancewa damu kana iya Rubuta Hausawa SIte a Google don samun sabbin rubuce – rubucenmu
Kayan da ake hada Alkaki da su
- Alkama (Ba’a so a wanketa da ruwa).
- sugar
- Tsamiya
- Kanwa
- Mai
Karanta
yadda mace zata zama tauraruwar girki
yadda ake fried rice
yadda ake yamball
Yadda ake hadin kayan hada Alkaki
Da farko dai za’a samu ita alkamar sai a bakace ta sannan bayan an yiu hakan sai a kai ta a wajen masu barji sai a barza ta ta sosai.
To bayan an barzata sai a sameta da daddare a zuba ,mata tsamiya a motsa su sosai su motsu sannan sai kuma a samu marfi a rufe kwabin da shi zuwa safe.
Da gari ya waye sai samu kanwa a zuba a cikin kwabin sai samu turmi a daka su ta yadda da kwabin alakmar da kuma kanwar su hade sosai.
Karanta:
Kamshin Girki: Abubuwa 10 da Ke Sa Kamshi da Dandanon Girki da Kuma Kyansa
Girki Adon Mace: Kala-kalar Girki da yadda zaki kware akan kirki don shine adon mata
Daga nan kuma sai a dora mai a cikin kasko yayi zafi sai a rika zubawa ana soyawa har sai sun soyu sai a kwashe a sa a mazubi bayan an gama sai a samu suga a soyashi wasu ma har lemun tsami suke sawa sidan ya soyu yayi ruwa sai a zuba a cikin alkakin da aka soya sai a ci.
Wasu Daga cikin Amfanin da Alkali yake a Jiki
- Yana kara gina jiki
- Yana taimakawa wajen inganta karfin jikin mutum
- Yana kara habbaka lafiyar mutum dalilin vitamins musamman a ruwan suga idan aka sa lemon tsami
- Abubuwa irin na alkama suna daga cikin abubuwan dake kara ma mata ni’ima.
Kammalawa
To a nan muka kawo karshen yadda ake hada alkaki sai a duba wasu sauran kayan girkin ko kuma na sanaoi domin amfana suma.
Idan akwai wata tambaya ko kuma wani karin bayani akan wannan post din ana iya yinsa a comment section da yake a nan kasa da mun duba muka gani zamo maido inshallahu mungode.
Author Profile

Latest entries
KasuwanciJanuary 14, 2025Noman Lambu: Bayani Akan Noman Lambu da Yadda Ake Yinsa
KasuwanciJanuary 14, 2025Solar da Yadda take aiki Gami da Yadda ake Hadawa
KasuwanciJanuary 14, 2025Yadda zaka yi amfani da Manhajar WPS office kyauta
Sana'o'iJanuary 6, 2025Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a