You are currently viewing Karin Kiba: Kunun Karin Kiba na Sabaya da Yadda Ake Yinsa

Karin Kiba: Kunun Karin Kiba na Sabaya da Yadda Ake Yinsa

Shin kana son kayi kiba? Koko kana da kiba karin kiba kakeso kayi? Kiba wani abu ce wadda take da amfani amfani sosai musammam ga wanda basu da ita suna son kodayaushe ace sun kara kiba, kuma idan tana madaidaiciya tana da amfani kamar yadda idan tayi yawa tana zama illa da cuta.

Kunu na daya daga cikin shahararrun abubuwan sha na gargajiya da ake sha a Najeriya, musamman a Arewacin kasar. Yana da dandano mai dadi kuma yana da matukar amfani ga lafiyar jiki. Amma ba kowane irin kunu ne ke kara kiba ba; yana da kyau a san yadda za a hada shi da sinadaran da ke taimakawa wajen samun nauyi.

A cikin wannan post din zamuyi magana akan yadda ake hada shi domin karin kiba tare bada shawarwari ga masu son suyi kibar.

Minene Kunun Karin Kiba na Sabaya Kuma Me Yasa Kunu Ke Taimakawa Wajen Karin Kiba?

Kunu na dauke da sinadaran gina jiki masu yawa kamar carbohydrates, mai, da furotin, wadanda ke kara kuzari da nauyi. Abubuwan da ake amfani da su wajen hada kunu kamar dawa ko masara suna cike da carbohydrates, wanda ke samar da makamashi ga jiki. Hakanan, idan aka hada kunu da madara, gyada, kwakwa, dabino, da zuma, yana kara nauyi da sauri.

Gyada na da yawan mai da furotin, wanda ke taimakawa wajen bunkasa jiki, yayin da madara ke kara kitsen jiki. Hakazalika, kwakwa da dabino suna ba da sinadaran kuzari da ke taimakawa wajen kara kiba cikin sauki.

Kunun Sabaya wani kunu ne wanda ya tattaro abubuwa da yawa da jiki yake so wanda yake sajikin mutum yayi kiba cikin dan karamin lokaci.

Kusan ma mutum idan yana shan sa cikin yan satuttuka ko watanni zai kara sa jikin sa yayi kiba.

Saboda abu ne kusan ya kunshi sinadaran da suke gina jiki sosai tare da ba jikin karafi da kuma kara masa lafiya da kuzari.

Hoton Kayan Hadin Kunun Karin kiba

Kayan Hadin na Sabaya

Wadannan sune kayan hadin da za’a sawo a kasuwa wanda ake hada shi kuma ga shi kamar haka zani lissafa su zamuyi misali da abu awo na gwangwani.

  • Shinkafa Gwangwani biyu 2
  • Gero Gwangwani 2
  • Alkama Gwangawani biyu 2
  • Gyada Gwangwani biyu 2
  • Ridi Gwangwani daya 1
  • Hulba rabin gwangwani 1/2
  • waken suya gwangawani daya 1

Yadda ake Hadawa

Bayan an tanadi kayan da muka ambata a sama sai a samu gero da alkama a sirfasu, bayan an gama sai a wankesu a rege saboda tsakuwar da suke da ita. sannan a shanya su su bushe. sai ki dauko wannan gyadar marar bawo sai a gyarata a soya ta sama sama yadda wannan bayan nata zai fita daga gareta.

Daga nan kuma sai a dauko ridi a gyara shi a wanke shi a sa shi ya bushe hakama a dauko shinkafa za’a wanketa a ki barta ta bushe, idan kuma ta hausa ce za’a fidda mata kazanta tsakuwa da sauransu.

waken suya ma za’;a gyara shi kana ki samu garin hulba ki hada da wadannan abubwan da muka ambataza’a nukasu.

Bayan an nuka su idan ana son amfani da su gaba ana iya sawa a rana garin ya bushe saboda in an tashi yi a gaba gudun kada ya lalace.

Idan za’a yi kiunun za’a dora ruwan zafi akan tukunya sai adama wannan garin kayan hadin sabaya din, sai a dama kamar yadda ake dama kunu, ana sa tsamiya ko kuma lemun tsami a ciki idan ana so yadda zai yi taste, sai adauko ruwan zafin da aka dora a tukunya a dama kunun kamar dai yadda ake dama kunu lafiya lau a sa sugar idan ana so a sha.

Karanta:Hanyoyin da ake bi Wajen Magance Cutar Diebities ciwon suga

Wannan hadin yana taimakawa sosai wajen saurin sa jiki kiba musammam ma idan mutum yana shansa sau biyu a kullun cikin karamin lokaci inshallahu zai yi kiba sosai kuma jikinsa zai yi kyau ya kara lafiya.

Karanta: Hanyoyin da ake bi Domin Rage Kiba

Yadda Ake Hada Kunu Mai Kiba Da Gina Jiki

Idan ana son samun kiba, yana da kyau a shirya kunu mai dauke da abubuwa masu yawa na kara nauyi. Ga yadda ake hada kunu mai kiba:

Abubuwan da Za Ku Bukata:

  • Dawa ko Masara – Domin samar da kuzari mai yawa (carbohydrates).
  • Gyada – Yana kara mai da furotin ga jiki.
  • Madara (Milk ko Nono) – Yana kara kitsen jiki da sinadarin calcium.
  • Zuma ko Sukari – Yana kara kuzari cikin sauki.
  • Citta da Kaninfari – Yana taimakawa wajen narkewar abinci da kuma samar da dandano mai kyau.
  • Kwakwa (Coconut Milk) – Yana da sinadarin mai da ke taimakawa wajen karin kiba.
  • Dabino (Dates) – Yana dauke da sinadaran kuzari masu kyau ga jiki.

Matakan Da Za A Bi Don Hada Kunu Mai Kiba

  1. A wanke dawa ko masara da kyau sannan a jika na tsawon awa 12 zuwa 24 domin ya yi laushi.
  2. A markada shi da ruwa tare da gyada, citta, da kaninfari domin inganta dandano da sinadaran jiki.
  3. A tace ruwan sannan a dafa har sai ya yi kauri.
  4. A bar shi ya huce, sannan a zuba madara, kwakwa, dabino, da zuma ko sukari domin kara masa dandano da sinadaran kuzari.
  5. A sanyaya shi a firinji domin samun sanyi da dadi a sha.

Tsarin Shan Kunu Domin Karin Kiba

1. Safiya (Breakfast)

Da safe, yana da kyau a fara rana da shan kofi biyu na kunu mai sanyi. Hakanan, ana iya cin biredi da mai ko kwakwa, da kwai mai gasasshe don kara sinadarai masu amfani ga jiki. Wannan na taimakawa wajen fara rana da kuzari sosai.

2. Rana (Lunch)

A lokacin rana, bayan cin tuwo da miyar taushe ko alale, yana da kyau a sha kofi daya na kunu domin kara kuzari. Hakanan, cin nama da kifi yana taimakawa wajen karin furotin. Ana iya hadawa da kayan itatuwa kamar ayaba da dabino domin kara lafiya da gina jiki.

3. Yamma (Dinner)

Da yamma, yana da kyau a sha kofi biyu na kunu tare da kosai ko waina. Hakanan, ana iya cin madara da kifi mai kitse domin karin kiba. Wannan na taimakawa wajen samun karin kuzari kafin kwanciya bacci.

4. Kafin Kwanciya (Before Bed)

Kafin kwanciya da dare, ana iya sha kofi daya na kunu mai zuma domin samun nauyi cikin sauri. Hakanan, shan madara da cin wake ko kuli-kuli yana taimakawa wajen kara furotin a jiki. Wannan na taimakawa wajen gina tsokoki da kara kiba.

shkarin kiba

Shawarwari Domin Samun Sakamako Cikin Sauri

  • A sha kunu mai dumi ko sanyi sau uku zuwa hudu a rana.
  • A guji shan abubuwa masu rage kiba kamar shayi ba sugar da abubuwan sha masu sinadaran rage nauyi.
  • A samu isasshen bacci na (7-9 hours) domin jiki ya sami damar kara nauyi cikin sauri.
  • A ci abinci mai yalwar carbohydrates da protein kamar shinkafa, doya, wake, da kuli-kuli.
  • A yi motsa jiki kadan don hana kiba mai lahani, amma kada a yi wuce gona da iri.

Wasu daga Cikin abubuwan da ke kara kiba

Wasu daga cikin abubuwan da suke taimakawa sosai wajen sa kiba sun hada da yawan shan madara lafiyayya da kuma cin abinci mai protein sosai kamar kifi.

sai kuma fannin abubuwan da keda calories sosai kamar su masara dawa, doya da sauran manyan abubuwa na carbohydrate kuma arika ciki sosai a koshi ba batun ci kadan.

Sai kuma samun isashhen baccin da motsa jiki kadan ba mai yawa ba yadda zai rika zubda kibarjiki.

Karanta: Hanyoyi 10 Domin Karin Kiba a Jikin Mutum

Amfanin kiba a jiki

Kiba tana da amfani sosai a jikin mutum wanda ga wasu daga cikinsu kamar haka

  • Tana taimakawa wajen kare jiki daga kwayoyin cuta
  • Tana Gyara jikin mutum yayi kyau in bata yi yawa ba
  • Tana sa jikin mutum ya zama mai karfi.
  • Tana taimakawa wajen kareshi daga yawan jin sanyi saboda akwai kitse a jikin

Karanta: 

Magunguna 5 da ya Kamata su Kasance Tare da Kai a Kullun

Amfanin Ruwa Dumi 5 ga Lafiyar Jiki

Maganin Ciwon Sickler da Kuma Bayani akan Cutar

Wasu Daga Cikin Muhimman Amfanin da sabaya yake karawa a Jiki

A cikinsa akwai carbohydrates irinsu gero wanda suke kara ma jiki sugar wanda shine yake taimakawa wajen gudanar da ayyukan dake cikin jikin mutum.

Bayan nan abu na biyu kuma akwai proteins kamar waken suya wanda yake kunshe da proteins mai yawan gaske yana saurin sa kiba da kyan jiki.

Daga nan kuma wani abu mai mahimmanci hulba da ke ciki wanda kowa yasan tana da matukar mahimmanci a jikin mutum musamman ma mata tana kyara masu fara da karin ni’ima.

Me Za’a Iya Tsammani Idan Kun Bi Wannan Tsarin?

Idan aka bi wannan tsarin shan kunu mai kiba, za a fara ganin canji a cikin watanni uku zuwa shida. A cikin shekara daya, za a iya samun nauyi sosai da kuma lafiyayyen jiki. Wannan tsarin yana da matukar amfani ga masu son kara kiba ba tare da amfani da magunguna ba.

 

 

Author Profile

Ibrahim Buhari
Ibrahim Buhari