Wainar Shinkafa ko masar shinkafa Abinci CE mai amfani da kuma dadi kuma yana kyau ace kin iyata saboda yawancin maza suna son uwar gida namasu waina in sun bukaci hakan a da farko zamu fara kayan hadin sannan muyi bayanin yadda ake hadata.
Table of Contents
KAYAN HADIN
- Farar shinkafa gwangwani
Wake rabin gwangwani
Sugar
Baking powder
yeast
Dafaffiyar Shinkafa
Gishiri
YANDA ZAA HADA KAYAN HADIN
Ga yadda akr hada kayan hadin dalla dalla a cikin matakai kamar haka
MATAKI NA DAYA 1
Dafarko dai Zaki jika shinkafarki, sai kuma a gefe daya kuma ki surfa wanken ki gwangwani days ki wanke shi sosai ( kamar yanda ake wankewa idan za a yi alale). Ya danganta da yawan shinkafar,idan har adadin shinkafar bai kai kwano1 ba kada a saka wake gwangwani1, sai a kwatanta waken da tafin hannu(Ana so shinkafarki ta kasance ta ninka waken sosai).
MATAKI NA BIYU 2
Bayan kin gama wanken sai ki hada tare da shinkafar ki saka yeast naki aciki ,idan kina buqatan kina iya sa kayan miya atta da albasa da tattasai in kings damage duk zaki iya sakawaa markado maki, already kin dafa a Shinkafarki sai ki zuba a cikin markadenda aka riga aka maki, ki saka gishiri da Dan sugar(idan ana buqatan hakan) ki juyasu su hade jikinsu ki ajiye kullun ya kumbura ko ya tashi.
MATAKI NA HUDU 4
Samo tanda mai kyau sai rika debo kullunki kina toyawa in shashen farko yayi ki juya day an ma ya soyu sai ki kwashe kiss a cikin kula ko plate shikenan.
Author Profile

Latest entries
KasuwanciJanuary 14, 2025Noman Lambu: Bayani Akan Noman Lambu da Yadda Ake Yinsa
KasuwanciJanuary 14, 2025Solar da Yadda take aiki Gami da Yadda ake Hadawa
KasuwanciJanuary 14, 2025Yadda zaka yi amfani da Manhajar WPS office kyauta
Sana'o'iJanuary 6, 2025Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a