Table of Contents
Yadda ake Farsfesun Nama
Assalamu Alaikum barka da ziyarto wannan shafi maialbarka, kamar yadda aka saba har kullun yau post din namu munzo ne akan yadda ake farfesu na nama wato (pepper souf) a turance wanda inshallah zani yi maku bayani gamsasshe akan yadda ake hada si.
To indai ba’a manta ta a bayanin a wannan website mai albarka wato Hausawa Site mun yi post akan yadda ake hada Cin-Cin, Cake, Fanke, Fried Rice da ma sauran nauka na girki kala-kala.
To bari mu fara lissafa kayan hadin da ake bukata wajen farfesu gasu kamar haka:
Kayan da Ake Bukata wajen Hadawa
Gasu Kamar Haka
- Nama
- Gishiri
- Man Gyada
- Thyme
- Kori
- Man ja
- Kayanj miya
- Ruwa
Karanta:
Yadda Ake Hadawa
Kayan da muka ambata a sama sune ake Bukata ga kuma yadda ake hada su su bada farfesu:
Da farko dai Idan kida yanka Namanki, sai ki sai ki dauraye shi ki rufe a gefe guda, sannan sai ki markade cefanenki ki hada da su citta, tafarnuwa da karamfani.
Dauko Naman da kika aje a dazu ki dora shi a saman tukunya ki dan sulalashi ko ki dafa shi, bayan ya dafu sai ki safke ki rufe shia gefe guda.
Daga nan kuma sai ki daura tukunya ki zuba mai da mai ki soya markadadden cefanenki, sai ki zuba ruwa ki motsa bayan nan kuma sai ki kawo maggi, gishiri ki zuba ki motsa su sai ki kulle ta dahu.
Daga nan kuma sai ki dauko wannan naman ki zuba bayan kin bashi mintunasai ki dauko thyme, kori citta da tafarnuwa,da karanfani wadanda aka daka sai ki zuba a cikin tukunyar,
Daga nan sai ki cigaba da motsasu saboda kar yayi kamu sai bashi mintuna shikenan sai ki samu kula ki zuba a ciki.
Author Profile

Latest entries
KasuwanciJanuary 14, 2025Noman Lambu: Bayani Akan Noman Lambu da Yadda Ake Yinsa
KasuwanciJanuary 14, 2025Solar da Yadda take aiki Gami da Yadda ake Hadawa
KasuwanciJanuary 14, 2025Yadda zaka yi amfani da Manhajar WPS office kyauta
Sana'o'iJanuary 6, 2025Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a