To dafarkode ana bukatar kitanadi Kayan hadi kamar haka
Table of Contents
Kayan hadin
- Offals (yanciki)
- Yam (doya)
- Thyme
- Curry
- Koren tattasai
- White pepper
- Black pepper
- Tarugu
- Mai
- Ruwa
- Albasa
- Gishiri
- Citta/tafarnuwa
- Bay leaf
Yadda zaki girka
Zaki fara wanke Kayan cikinki wato (offals) da ruwan zafi sufita sosai.
Sai ki zuba Kayan kamshi tareda albasa wato thyme, curry, black pepper, white pepper, gishiri, citta, tafarnuwa sai ruwa dai-dai gwargwado kimotsa

Sai kikulleshi yadan sulala.
To yanzu kuma saiki fera doyarki ki daddatsata kanana kiwanketa.
Sai kizubata atukunya kisa ruwa da gishiri tadahu.
Bayan doyarki tadahu, sai ki zuba mai acikin kasko ko tukunya tare da albasa yasoyu.
Saiki zuba wannan doyar dakika sulaka aciki tasoyu sannan kitsameta.
To bayan nan kuma sai ki dauko offals dinki dakika tanana (yanciki) suma kisoyasu acikin man.
Bayan kinsoyasu duka sai ki rage Manda kikayi amfani dashi kibar dede Wanda ze isheki sanwa.
Sannan ki zuba albasa, tarugu, citta/tafarnuwa, thyme, curry, cumin, bay leaf da pepper mix.
Kisoyasu natsawon minti biyar amma kada kisa wuta dayawa.
Bayan yasoyu sai ki zuba soyayyun offals dinki da doya sai koren tattasai ki motsa kamar tsawon minti biyu kingama.
Author Profile

Latest entries
KasuwanciJanuary 14, 2025Noman Lambu: Bayani Akan Noman Lambu da Yadda Ake Yinsa
KasuwanciJanuary 14, 2025Solar da Yadda take aiki Gami da Yadda ake Hadawa
KasuwanciJanuary 14, 2025Yadda zaka yi amfani da Manhajar WPS office kyauta
Sana'o'iJanuary 6, 2025Koyon Sana’a: Muhimman Abubuwan Dubawa kafin koyon sana’a